Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya amince da kafa sabuwar rundunar masu tsaron dazuka domin dakile matsalar rashin tsaro da ke ƙara kamari a sassa daban-daban na ƙasar. Wannan mataki zai haɗa da ɗaukar ma’aikata fiye da dubu ɗari da talatin, waɗanda za su rika tsaron dazuka sama da 1,129 da ake da su a faɗin Najeriya.
Wannan tsari na musamman an amince da shi ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Ƙasa da aka faɗaɗa, wanda aka gudanar a ranar Litinin. Ana sa ran kowace jiha za ta ɗauki daga mutum 2,000 zuwa 5,000 bisa ƙarfin kuɗinta da yawan dazukan da take da su.
Za a gudanar da horar da sabbin jami’an tsaron dazukan tare da sanya idanu daga Ofishin Mai ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro da kuma Ma’aikatar Muhalli. Wadannan jami’ai za su kasance masu kayan aiki na zamani da horo na musamman.
Mai ba Shugaban Ƙasa shawara kan Harkokin Yada Labarai da Sadarwa, Sunday Dare, ne ya bayyana hakan a shafinsa na X a ranar Laraba. Ya bayyana cewa gwamnati ta kafa rundunar ‘yan tsaron dazuka a hukumance don ƙarfafa tsaro a ƙasar.