Gwamna Namadi ya taya shugabannin ‘yan jarida murna bisa nasarar da suka samu a zaben da aka gudanar

0 137

Gwamna Umar Namadi ya taya sabbin shugabannin kungiyar ‘yan jarida ta kasa reshen Jihar Jigawa, murna bisa nasarar da suka samu a zaben da aka gudanar.

A wata sanarwa da sakataren yada labaran gwamnan Hamisu Mohammed Gumel, ya fitar, Gwamna Namadi ya yaba da yadda aka gudanar da zaben cikin lumana, inda ya bayyana shi a matsayin sahihin zabe

Gwamnan ya kuma yaba da rawar da ‘yan jarida ke takawa wajen kare ‘yancin fadar albarkacin baki da kuma ci gaban sana’ar aikin jarida, tare da jinjinawa kungiyar NUJ bisa kokarinta na ci gaba da kare mutuncin aikin jarida a jihar da kasa baki daya.

Malam Namadi ya bukaci sabbin shugabannin NUJ da su kiyaye da ka’idojin aikin jarida.

Ya kara da tabbatar musu da goyon bayan gwamnatinsa ga ‘yancin aikin jarida, tare da bukatar samar da yanayi da zai ba su damar gudanar da ayyukansu cikin ‘yanci da kuma alhakin aiki.

Leave a Reply