Babbar Kotun Jiha ta soke wata kara ta aikata laifin fyade da alfasha da akayi a karamar hukumar Jahu
Babbar Kotun Jiha mai lamba hudu ta soke wata kara ta aikata laifin fyade da alfasha da ake tuhumar Ibrahim Alfa daga kauyen Garado dake karamar hukumar Jahun da wasu mutane biyu a karkashin Sashe na 3(1) na Dokar Hana Cin Zarafin Mutane ta Jihar Jigawa.
An zargi wadanda ake tuhuma da aikata wannan mummunan laifi akan ’yar shekaru 12 da haihuwa, wadda take ’ya ce ta haihuwa ga wanda ake tuhuma na farko.
Laifin ya saba da Sashe na 3(1) kuma hukuncinsa yana karkashin Sashe na 3(4) da 5(2) na Dokar VAPP mai lamba 2 ta Jihar Jigawa, 2021.
Sai dai, fiye da shekaru uku, masu gabatar da kara sun kasa gurfanar da wadanda ake zargi a gaban kotu, lamarin da ya haddasa tsaiko mara amfani a shari’ar.
Alkali mai shari’a ya jaddada cewa kotu ba za ta ci gaba da sauraron kara ba idan masu kara ba su nuna jajircewa wajen ganin an samu adalci ba.