An Ƙaddamar Da Kotun Sauraron Ƙarar Zaɓen Ƙananan Hukumomi Da Za’ayi Ranar 29 Ga Yuni A Jigawa

0 173

Babban alkalin alakalai na jihar Jigawa Aminu Ringim ya kaddamar da kotun sauraron korafe korafen zaben kananan hukumomi da za’ayi a ranar 29 ga watan Yuni.

Da yake kaddamar da kotunan a Dutse ya bayyana cewa samar da kotunan na kunshe ne cikin dokar hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta shekara 2012.

Ya bayyana cewa kotun korafe korafen tana da karfin sauraron karbar dukkanin wasu korafe korafen da suka shafi zabe batare da katsalandin wata kotu ba.

Mai shari’a Aminu Ringim ya ce kotun tana da ofis ofis a yankunan Dutse, Hadejia, da kuma Ringim.

Ya kuma ce shelkwatar kotun zata kasance a Dutse babban birnin Dutse.

Leave a Reply

%d bloggers like this: