Jami’an Tsaro Sun Samu Gagarumar Nasara A Bauchi

0 204

Hukumar tsaro ta farin kaya ta jihar Bauchi ta damke wasu mutane biyar da ake zargin su da satar wayoyi na wutar lantarki da kudinsu ya kai Naira milyan 5.4

Kwamandan rundunar a jihar Halliru Usman ya bayyana hakan yayin da yake gabatar da wadanda ake zargin a gaban yan jaridu.

Ya ce daga cikin wadanda ake zargin akwai mai suna Sanusi Ibrahim dan shekaru 20, da Mansur Hussaini dan shekaru 25 da kuma Aminu Hassan dan shekaru 26 dukkanin su yan asalin garin Tudun Salmanu a jihar ta Bauchi.

Ya ce ofishin jami’an su dake karamar hukumar Dass ne ya damke wadanda ake zargin a ranar 25 ga watan Yuni 2019.

Kazalika ya ce za su meka wadanda ake zargin gaban kotu da zarar an kammala bincike.

Leave a Reply

%d bloggers like this: