Gwamnatin Yobe Ta Yiwa Jarirai Da Masu Juna Biyu Gata

0 111

Gwamnatin jihar Yobe ta kaddamar da shirin makon kula da kananan yara da mata masu juna biyu.

Gwamnan jihar Alhaji Mai-Bala-Buni wanda ya samu wakilcin mataimakinsa, Alhaji Idi Gubana ya ce manufar wannan shiri shi ne bunkasa harkokin lafiyar kananan yara da mata masu juna biyu a fadin jihar.

Buni ya ce Gwamnatin jihar tana daidaita abubuwa da basu gudummawa a bangarori da dama.

Ya kara da cewa biyan wadanda ke gudanar da aikin kan lokaci kamar yadda tsohuwar Gwamnatin data gabata tayi ya taimaka wajen samun nasarar aikin.

Sakataren ma’aikatar lafiya ta jihar Alhaji Hamid Alhaji, ya ce shirin kula da lafiyar kananan yara da mata masu juna biyu dake gudana a jihar ana sa ran zai samu kashi 90 cikin dari yayin gabatar da shirin.

Wakilin hukumar lafiya ta duniya Adamu Baffale ya yabawa gwamnatin jihar wajen kokarinta na ganin an samu nasarar shirin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: