An cafke wasu Maniyyata a filin jirgin samada suka hadiye kwayoyin cocaine guda 90 a Kano

0 209

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta cafke wasu maniyyata guda biyu a filin jirgin sama na Mallam Aminu Kano a Kano, bayan da aka gano sun hadiye kwayoyin cocaine guda 90.

Bisa sahihan bayanai, jami’an hukumar sun dakatar da su a lokacin dubawa ta ƙarshe, inda daga bisani aka gano gram 1.04 na kwayoyin a cikin jikinsu.

Hukumar ta ce ta rushe wata ƙungiya da ake zargin tana amfani da aikin hajji a matsayin hanyar safarar miyagun kwayoyi, inda aka kama wasu mutum uku da ake zargin su ne manyan shugabannin aika-aikar.

Bugu da kari, hukumar ta kama wani attajiri mai shekaru 60 dauke da wraps 65 na cocaine a hanyar sa ta zuwa Iran, da kuma kama codeine da wasu magungunan opioids da kudinsu ya kai biliyan ₦9.3 a Fatakwal, kudaden jabu a Kano, tabar wiwi fiye da buhu 400 a Adamawa, da kuma wani fitaccen dillalin kwayoyi a jihar Kwara.

Leave a Reply