Ana sa ran ruwan sama mai yawa musamman da safe da yamma a jihohin Najeriya da dama – NiMET

0 210

Hukumar hasashen yanayi ta kasa, NiMET, ta fitar da rahoton gargaɗi kan hadurran guguwar iska da ruwan sama daga Litinin zuwa Laraba a yawancin sassan ƙasar, inda jihohin Arewa irin su Taraba, Kaduna da Kano za su fi fuskantar tasirin farko.

Yankunan tsakiyar ƙasa ciki har da babban birnin tarayya, Jihar Neja da Nasarawa ana sa ran ruwan sama mai yawa musamman da safe da yamma, yayin da jihohin kudu kamar Ondo, Rivers da Akwa Ibom za su fuskanci yanayi na damina da gajimare.

Hukumar ta shawarci jama’a da su yi taka-tsantsan da iska mai ƙarfi da ka iya janyo ankuwar da hadurra, tare da jan kunne kan gujewa tafiya da mota a lokacin ruwan sama da cire na’urorin lantarki don kauce wa guguwa da walƙiya. Hukumar ta kuma bukaci kamfanonin jiragen sama da su nemi karin bayani kan yanayin filayen sauka da tashin jirage, yayin da hukumomi ke bukatar da karin lura da bin ka’idojin tsaro.

Leave a Reply