Sama da yara marayu mata da maza 31 ne suka amfana da sabbin tufafin kayan sallah wanda kungiyar QAFILATUL MAHABBAH ta kasa reshen Karamar hukumar Ringim ta raba karkashin aiyukan ta na farantawa marayu da masu karancin gata a fadin yankin.
Daya daga cikin shugabannin kungiyar na kasa kuma kwamishinan makamashi da lantarki na jihar jigawa Engeener Surajo A Musa yace kungiyar tana gudanar da rabon tufafin kayan sallah ne ga yara marayu da nufin sanya farin ciki a zukatansu.
Ya ce kungiya tana karkashin jagorancin babban limamin masallacin kasa dake Abuja kuma tana gudanar da aiyukan taimakon marayu da ciyar da Alumma a lokacin azumin Ramadan da kai ziyara asibitoci da gidajen gyaran hali da shirya tarurrukan wayar da aluma da ilimantar dasu ilimin addinin musulunci. Yace a halin yanzu kungiyar tana da rassa guda biyar a fadin jihar jigawa da kuma rassa sama da 48 a fadin kasar nan. Kayayyakin da aka raba sun hada da sabbin rigunan yara maza da na mata inda sama da marayu 31 suka amfana.