Gwamnatin Tarayya ta bayar da 6 da kuma 9 ga wata a matsayin hutun Babbar Sallah

0 77

Gwamnatin Tarayya ta bayyana Juma’a, 6 ga Yuni da Litinin, 9 ga Yuni, 2025 a matsayin ranakun hutu domin murnar bikin Babbar Sallah na bana.

Ministan Harkokin Cikin Gida, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a madadin Gwamnatin Tarayya a wata sanarwa da Babbar Sakatariyar Ma’aikatar, Magdalene Ajani, ta fitar a jiya Litinin.

Tunji-Ojo ya taya dukkan al’ummar Musulmi na cikin gida da na ƙasashen waje murnar wannan lokaci mai albarka.

Ya yi kira ga al’ummar Musulmi da su ci gaba da nuna kauna ƙwazo, sadaukarwa da gaskiya kamar yadda Annabi Ibrahim (A.S) ya nuna. Haka kuma ya bukace su da su yi amfani da wannan dama wajen yin addu’a domin samun zaman lafiya da ci gaban kasa.

Ministan ya bukaci ‘yan Najeriya da su mara wa wannan gwamnati baya wajen ƙoƙarinta na dawo da martabar Najeriya a matsayin ƙasa mai girma.

Leave a Reply