Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin farfado da masana’antar koko(Cocoa) ta kasa

0 183

Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin farfado da masana’antar koko ta kasa da kuma raya dukkan harkar noma a ƙasar nan.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Sen Kashim Shettima, ne ya bayyana haka a ranar Litinin yayin da yake karɓar wata tawaga daga World Cocoa Foundation (WCF) a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya bayyana cewa shugaban tawagar, Chris Vincent, ne ya jagoranci tawagar.

Shettima ya sake jaddada kudirin Gwamnatin Shugaba Bola Tinubu na mayar da Najeriya ƙasar da ke samar da koko zuwa ƙasa mai sarrafa koko domin kasuwannin duniya.

Ya bayyana cewa Majalisar Zartarwa ta Ƙasa (FEC) ta amince da ƙirƙirar Hukumar Gudanar da Koko ta Ƙasa (NCMB) don tallafa wa shirin farfado shi a wannan fanni. A cewarsa, gwamnati na mai da hankali wajen bunƙasa noman koko da kuma kare gandun daji, tare da ƙara darajar koko ta hanyar sarrafawa a gida.

Leave a Reply