Gwamnatin Jihar Oyo ta rage farashin raguna, shinkafa da man girki ga ma’aikatan gwamnati a jihar, a wani yunƙuri na sauƙaƙa wa ma’aikatan Musulmi kafin bikin Babbar Sallah.
Shugaban Hukumar Lamunin Noma na Jihar Oyo, Sheikh Taofeek Akeugbagold, ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Ibadan, yayin rabon kayan ga wasu daga cikin masu cin gajiyar shirin.
A cewarsa, ma’aikata sama da 2,500 ne za su ci gajiyar wannan tsari da gwamnati ta ƙirƙiro.
Sheikh Taofeek ya bayyana cewa wannan shiri na tallafi an tsara shi ne domin rage wa ma’aikata raɗaɗin halin mastin tattalin arzikin ƙasar.
Ya ƙara da cewa za a ci gaba da raba kayayyakin har zuwa ranar 4 ga Yuni, karkashin jagorancin Gwamna Seyi Makinde.
Shugaban ya kuma bayyana cewa biyan kudin kayan da aka ragesu zai kasance cikin sauƙi, inda za a cire bashin cikin kashi uku daga albashin ma’aikatan, daga watan Agusta. Wasu daga cikin ma’aikatan da suka amfana sun yaba wa gwamnatin jihar bisa wannan shiri, suna cewa wannan mataki ya dace kuma ya zo a kan gaba.