Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Alhaji Aliko Dangote, ya bayyana cewa ‘yan Najeriya na biyan kashi 55 cikin dari ne kawai na farashin fetur idan aka kwatanta da abokan zamansu a wasu kasashen yammacin Afirka, sakamakon tasirin matatar man sa da ke sayar da fetur tsakanin ₦815 zuwa ₦820 akan kowace lita.
Yayin da shugaban kungiyar ECOWAS, Dr Omar Touray, ya kai ziyara ga matatar mai mai fitar da ganga dubu 650 a rana, Dangote ya bayyana yadda hakan ke rage farashin dizel da kuma saukaka kudin samar da kayayyaki ga sassan noma da hakar ma’adanai.
Dangote ya kara da cewa lokaci ya yi da Afirka za ta dogara da kanta wajen sarrafa albarkatunta, yana mai musanta zargin da ke cewa matatar ba za ta iya cika bukatun yankin ba.
Jami’an ECOWAS sun yaba da wannan gagarumin aiki a matsayin alamar fata ga Afirka, tare da yin kira da a karfafa hadin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu domin bunkasa masana’antu a nahiyar.