Tinubu yayi alkawarin daidaita tsaro a lokacin daya karbi Shugabancin Najeriya a shekarar 2023

0 221

An bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya hau kujerar shugabancin kasa ne tare da alƙawarin daidaita harkar tsaro a cikin shirin sa na ajandar sabunta fata, amma duk da haka matsalolin tsaro sun ci gaba da ta’azzara a faɗin ƙasar, lamarin da ke barazana ga zaman lafiya da kuma cigaban ƙasa.

Sai dai tun bayan shan rantsuwar da yayi alkawarirrikan da suka hada da na gyaran matsalar tsaron a ranar 29 ga watan mayun 2023, hare-haren ƴan ta’adda da ƴan bindiga sun ƙaru musamman a yankunan karkara inda aka kashe dubban mutane, wasu kuma suka shiga hannun masu garkuwa da mutane. Duk da kiran da shugaba Tinubu ya ke kira ga hafsoshin tsaro da su kawo ƙarshen kisan jama’a, hare-haren sun ci gaba da ƙaruwa da sauyawa fasali, lamarin da ke bayyana cewa barazanar tsaro ba abu ne da za a warware cikin sauƙi ba, sai da cikakken tsarin aiki da haɗin kan al’umma.

Leave a Reply