Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da aka dakatar, na shirin gurfana a gaban kotu a gobe Talata domin fuskantar tuhumar batanci da gwamnatin tarayya ke yi mata, biyo bayan zarge-zargen da ta yi cewa shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello na da hannu a yunkurin kasheta.
Tuhumar na da nasaba da wani shirin talabijin da kuma wata tattaunawa ta waya, inda ake zargin Sanata Natasha da alakanta Akpabio da wani rikici na cire sassan jikin marigayiya Iniubong Umoren.
Lauyanta, West Idahosa, ya tabbatar da cewa sanatar za ta halarci zaman kotun tare da jaddada cewa za ta mutunta tsarin shari’a, duk da rashin tabbas kan ko gwamnati za ta fara shari’ar kai tsaye.
Masana na ganin cewa tunda akwai Akpabio, Yahaya Bello da wasu fitattun mutane a matsayin shaidu, ana ganin shari’ar za ta janyo karin haske da cece-kuce a fagen siyasa da shari’a a Najeriya.