An gano wasu matasa da ke yunkurin tayar da tarzoma a lokacin bukukuwan Sallah

0 207

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta ce ta gano wasu matasa da ke yunkurin tayar da tarzoma a lokacin bukukuwan Sallah.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Muhammad Usaini Gumel ne ya bayyana haka a wata ganawa da ya yi da malaman addinin musulunci da kuma wakilai daga masarautun jihar kano guda biyar a jiya Litinin.

Sai dai ya bayar da tabbacin cewa ‘yan sanda sun yi gaggawar daukar mataki kan masu aikata laifukan da ke kokarin karya doka da oda domin tayarda husuma lokacin da kuma bayan bikin Eid-el-Fitr. Ya bayyana Kano a matsayin jiha daya tilo da babu daya daga cikin ‘yan jihar da masu garkuwa da mutane ko ‘yan fashi ke tsare da shi, yana mai alakanta hakan da sa-idon daga jami’an tsaro.

Leave a Reply

%d bloggers like this: