Bello Bodejo ya musanta alakanta Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da halin da yake ciki

0 110

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore da ake tsare da shi, Bello Bodejo ya musanta alakanta Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa da halin da yake ciki a yanzu a hannun hukumomin tsaro.

Bodejo, wanda yayi magana ta bakin lauyansa, Mohammed Sherif a jiya Litinin, ya ce har yanzu bai yi wata magana ba a yayin da yake tsare a hannun hukumar leken asiri.

Ya mayar da martani ne ga wata kafar yada labarai da ta alakanta gwamnan da laifin da ake zarginsa da shi.

Sheriff ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar manema labarai da ya sanyawa hannu kuma ya rabewa manema labarai a Abuja. Bodejo wanda ke fuskantar tuhume-tuhume uku na ta’addanci, an ruwaito a cikin sanarwar yana mai  ikirarin cewa gwamnan ya matsa masa ya kafa kungiyar ‘ Zaman lafiya wadda tayi sanadiyar kama shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: