An kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne guda 7 tare da kwato bindigogi a jihar Kaduna

0 90

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta ce jami’anta sun kama wasu da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne guda bakwai tare da kwato bindigogi a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Mansir Hassan, ne ya sanar da kama su a wata sanarwa da ya fitar yau Talata a Kaduna.

A cewar Hassan, kamen zai zama wani babban cikas ne ga kungiyoyin masu aikata laifuka a jihar, yayin da rundunar ke ci gaba da samun gagarumar nasara wajen tabbatar da tsaro ga dukkan ‘yan kasa.

Ya bayyana cewa an fara aikin ne a ranar 6 ga watan Afrilu bisa bayanan sirri da aka samu daga wata majiya mai tushe. Ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ali Audu, ya yaba da hadin kai da kuma taka tsan-tsan da al’umma suka nuna wajen bayar da muhimman bayanai da suka kai ga nasarar gudanar da wannan aiki.

Leave a Reply

%d bloggers like this: