Wasu ‘yan sa kai da dama sun rasa rayukansu a wani artabu da ‘yan bindiga a unguwar Dogon-Dawa da ke karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.

0 140

Wasu ‘yan sa kai da dama sun rasa rayukansu a wani artabu da ‘yan bindiga a unguwar Dogon-Dawa da ke karamar hukumar Mariga ta jihar Neja.

Majiyoyi a yankin sun ce lamarin ya faru ne da safiyar ranar Asabar lokacin da ‘yan bindigar suka yi yunkurin kai hari kan al’ummomin yankin.

An ce ‘yan sa kan sun bi sahun ‘yan bindigar zuwa maboyar su, inda suka yi musu kwanton bauna.

Majiyoyi sun ce an kuma samu asarar rayuka a bangaren ‘yan bindigar sai dai ba’a iya tantance adadin wadanda suka mutu a bangarensu ba. Shugaban karamar hukumar Mariga Abbas Kasuwar Garba ya tabbatar da faruwar lamarin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: