An kaddamar da wani shiri na gwajin cutar HIV na kai-da-kai

0 438

Kasar Ghana ta kaddamar da wani shiri na gwajin cuta mai karya garkuwar jiki na kai-da-kai a wani bangare na kokarin dakile yaduwar cutar a kasar.

shirin zai ba wa ‘yan Ghana damar duba matsayinsu a sirrance.

Ɗaya daga cikin damar da aka bayar, gwajin HIV na kai-da-kai, ya haɗa da shafan haƙora na sama da na ƙasa.

Sai dai hukumomi sun ce dole ne a tabbatar da sakamakon da aka samu a cibiyar lafiya.

Hukumar Agaji ta Ghana ta bayar da rahoton cewa, akwai sama da mutane 350,000 da ke dauke da cutar a kasar, amma kashi 71% ne kawai suka san halin da suke ciki. An yi maraba da bullo da  shirin wadanda suka bayyana shi a matsayin mai yuwuwar kawo sauyi wajen bunkasa ayyukan gwajin cutar kasar a Ghana.

Leave a Reply

%d bloggers like this: