An kama fiye da mutum 300 da ake zargin ƴan bindiga ne a jihar Kaduna

0 253

Kamar yadda BBCHausa ta wallafa; rundunar ƴan sandan Najeriya reshen Jihar Kaduna ta bayyana cewa a bana ta kama mutum 305 da take zargi da fashi da makami da garkuwa da mutane a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna da wasu sassan jihar.

Hakazalika ta kuma ce ta gurfanar da mutum 242 a kotunan jihar. Ta kuma ce ta kama muggan makamai 161 da kuma harsasai 2,924 daga wurin masu laifi duk a bana.

Rundunar ta kuma ce ta ceto mutum 168 waɗanda aka yi garkuwa da su inda aka sada su da iyalansu.

Ƴan sandan sun kuma musanta zargin da mataimakin kakakin majalisar wakilai Honourable Ahmed Idris Wase ya yi cewa ƴan sanda na da hannu a garkuwa da mutane da fashi da makami da ake yi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: