Sojojin Faransa sun bar birnin Timbuktu bayan shafe shekaru 9 suna taimaka wa sojojin Mali domin kwato garin daga hannun masu ikirarin jihadi
Sojojin Faransa sun bar birnin Timbuktu, bayan sun shafe shekaru 9 suna taimaka wa sojojin Mali domin kwato garin daga hannun masu ikirarin jihadi.
Janyewar tana da tasiri matuka ganin cewa a birnin ne tsohon Shugaban Faransa Francois Hollande ya kammala shirye-shiryen sojojin Faransa su shiga Mali domin taimako.
A jiya, wani janar din soji ya mika wani mukulli na katako ga wani sojin Mali kafin dakarun na Faransa su janye daga sansaninsu.
A hankali Faransa na ta rage dakarunta daga arewacin Mali, sakamakon barazanar masu ikirarin jihadi.
Dangantaka ta yi tsami tsakanin gwamnatin Mali da ta Faransa tun bayan juyin mulkin da aka yi a Malin a bara.