An kama jami’in dan sandan da ake zargi ya harbe wani matashi da ke talla a Kasuwar wuse

0 169

Rundunar ‘yan sandan Abuja ta ce ta kama Usman Ishaya Magaji, jami’in dan sandan da ake zargi ya harbe Ibrahim Yahaya wani matashi da ke talla a Kasuwar wuse a ranar Talata.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Abuja, SP Adeh Josephine ce ta tabbatar da kamen, ta wayar tarho ga wakilinmu da yammacin ranar Talata.

SP Josephine ta ce wanda ake zargin yana hannun ‘yan sanda a halin yanzu, kuma za a ci gaba da bincike.

Manema labarai sun ruwaito cewa wasu fusatattun matasa da yammacin ranar Talatar sun kona wasu sassa na kasuwar Wuse da ke Abuja, ciki har da wasu motoci da aka ajiye a cikin kasuwar, bayan da ‘yan sanda suka harbe matashin mai shekaru 17. An ce marigayin da ake tuhuma a kotun tafi-da-gidanka da ke cikin kasuwar ya yi yunkurin tserewa, inda nan take ‘yan sanda suka harbe shi, kuma nan take ya ce ga garinku.

Leave a Reply

%d bloggers like this: