An kama wani gardi da ya yi shigar mata a dakin kwanan ɗalibai mata a jihar Kano

0 252

Jami’an Hukumar tsaron Fararen Hula, wanda aka fi sani da ‘Civil Defence’ a jihar sun cafke mutumin mai suna Muhammad Munzali daga Kaura Gidan Damo a karamar hukumar Shanono a jihar.

Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Ibrahim Abdullahi, ya tabbatar da kama wanda ake zargin a wata sanarwa a jiya Juma’a.

Ya ce Jami’an hukumar ne suka cafke wanda ake zargin da misalin karfe 10 na dare a ranar Laraba a lokacin da yake kutsawa cikin dakin kwanan dalibai mata na jami’ar Skyline Nigeria, da ke kan titin Sardauna Crescent, Nassarawa GRA, jihar Kano.

A cewar Abdullahi, ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin kutsawa cikin dakin kwanan dalibai na jami’a mai zaman kan ta, inda daga nan sai a dauki mataki na gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: