Gwamnatin jihar Yobe zata ciyar da musulmi masu karamin karfi da mabukata dubu 16,800

0 157

Gwamnatin jihar Yobe ta ce musulmi masu karamin karfi da mabukata dubu 16 da dari 800 ne za su ci gajiyar shirin buda baki a cikin watan Ramadan.

Kwamishinan al’amuran Addini na Jihar Alhaji Yusuf Umar shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Damaturu yayin rabon kayan abinci ga masu aikin kwangilar samar da abincin.

Kwamishinan ya ce shirin ciyarwa a watan Ramadan zai lakume sama da Naira miliyan dari. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar ta fadada cibiyoyin ciyar da abinci daga 67 zuwa 84 kuma ana sa ran kowace cibiya zata ciyar da akalla mutane dari biyu a kullum

Leave a Reply

%d bloggers like this: