Hukumar Kwastam ta kama wasu makamai da kakin sojoji a tashar Tin-Can Island

0 113

Hukumar Kwastam ta kama wasu makamai da kakin sojoji a tashar Tin-Can Island da ake zargin wasu tawagar masu aikata laifuka ne suka shigo da su cikin ƙasar nan ta ɓarauniyar hanya.

Daga cikin abubuwan da aka kama sun haɗa da kakin sojoji da miyagun ƙwayoyi irin su Colorado.

Makaman da aka kama sun haɗa da bindigogi masu sarrafa kansu da kuma wasu nau’in bindigogin.

Kawo yanzu dai ba a bayyana ko an kama wani da ake zargin da hannu a shigo da kayayyakin ba Kwanturolan hukumar ta Kwastam, Mista Adewale Adeniyi, ya shaida wa manema labarai a lokacin cewa an kama wasu mutane biyu da ake zargi da hannu wajen kama su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: