‘Yan majalisar dokokin Kenya suna gudanar da bincike a kan daukar ma’aikatan haraji

0 116

‘Yan majalisar dokokin Kenya suna gudanar da bincike a kan daukar ma’aikatan haraji, bayan da ta bayyana cewa an ki daukar wasu bayan da aka yi musu gwajin cuta mai karya garkuwar jiki da kuma gwajin juna biyu.

Hukumar haraji ta kasar ta ce, ta ki amincewa da sama da mutum 130 da suka nemi aikin na tattara haraji, bayan da aka yi musu gwajin a shekarar da ta wuce.

Daukar aikin na daga yunkurin gwamnatin kasar na kara samun kudade, da kuma maganin masu kin biyan haraji. Hukumomin kasar ta Kenya sun ce aikin na daukar masu karbar haraji, aiki ne da yake bukatar mutane masu karfi da azama da kuma cikakkiyar lafiya, saboda haka duk wanda aka dauka sai an ba shi horo na soja, saboda kalubalen da ke tattare da aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: