Gwamnatin tarayya ta fara rarraba mitocin wutar lantarki a barikin sojoji dake fadin kasar nan

0 92

A wajen kaddamar da shirin da aka yi a hedikwatar birgediya ta 9 ta rundunar sojojin Najeriya, dake karamar hukumar Ikeja a karshen mako, ministan wutar lantarki, Adebayo Adelabu, ya ce atisayen zai kawo karshen lissafin kudi a fannin wutar lantarki.

Adelabu ya kara da cewa shirin zai soma ne a barikin soji dake Ikeja inda yace shine kashi na farko na shirin, wanda yace shiri zai dauki tsawon makonni shida kafin a soma kashi na biyu. Ya bayyana cewa a wannan shirin da ake yi a yanzu an fitar da zunzurutun kudi har Naira biliyan 12.7 daga cikin jimillar Naira biliyan 40 na aikin rarraba mita ga jama’a.

Leave a Reply

%d bloggers like this: