An kama wani matashi da buhunan tabar Wiwi 45

0 115

Rundunar ‘yansanda sun yi nasarar kama wani matashi mai suna Muhammad Ismail mai shekaru 30 da buhunan tabar Wiwi 45 da wasu kwayoyi a karamar hukumar Malunfashi ta jihar Katsina

Da yake yi wa manema labarai jawabi, kakakin rundunar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya bayyana cewa sun samu wannan nasara ne ta hanyar samun bayanan sirri.

Ya Kuma kara da cewa wanda ake zargin yana zaune ne a unguwar B.C.G.A a garin Malunfashi ta jihar Katsina

Yace lokacin da jami’an su suka samu labari ba su yi kasa a gwiwa ba, inda nan take baturen ‘yansanda na Malunfashi ya hada jami’an su domin kama wadanda ake zargi. A cewar ASP Abubakar Sadiq Aliyu an kama wanda ake zargi da buhunan tabar wiwi guda 45 da kwalabe 500 na kayan maye da kwaya mai suna D5 duk a tartare da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: