Hukumar NYSC ta musanta hallaka mai hidimtawa kasa

0 106

Hukumar mata yan yiwa kasa Hidima ta NYSC ta karyata wani labarin da ke yawo a kafafen sada zumunta na wani dan yiwa kasa Hidima da yan bindiga suka hallaka akan hanyar sa daga kaduna zuwa Katsina a lokacin da ya dawo domin tantancewar wata-wata.

A cikin wani bayani mai dauke da sa hannun Daraktan yada labarai da Hulda da jama’a na Hukumar Eddy Megwa, yace ga dukkanin binciken da sukayi sun gano labarin ba gaskiya bane.

Bayanin ya kara da cewa Dan yiwa Kasa Hidiman Mamudo Sa’idu Obaje, yana aikin yiwa kasa Hidima ne a makarantar kwalejin yan mata dake Katsina.

Bayanin ya kuma ci gaba da cewa, matashin yana kan hanyar Kaduna ne zuwa Katsina inda ya hadu da hatsarin mota a garin Gayaza dake karamar hukumar Kankia a jahar Katsina, tare da sauran fasinjoji. Hukumar ta NYSC ta mika sakon ta’aziyya ga iyalan matashin wanda ya rasu a lokacin da yake aikin yiwa kasa Hidima.

Leave a Reply

%d bloggers like this: