An kama wasu mutane uku da ake zargi da kashe wakilin VON

0 245

Rundunar ‘yansandan jihar Zamfara ta sanar da kama wasu mutane uku da ake zargi da kashe wakilin VON, Hamisu Danjibgan, Haruna Danjibga tare da wadanda ake zargin sun sayi kadarorin da aka kwashe bayan sun kashe marigayin.

Wadanda ake zargin a cewar rundunar ‘yansandan, su ne Mansur Haruna wanda ya kasance dan uwan marigayin ne da kuma abokinsa Ibrahim Nababa da kuma wanda ya sayi dukiyar marigayin da aka sace kuma dukkansu sun amsa laifin kashe Danjibga.

Da yake gabatar da wadanda ake zargin, kwamishinan ‘yansanda, CP Mohammed Shehu Dalijan, ya ce da muka samu rahoton kashe dan jaridan, Hamisu Danjibga, ‘yansanda sun dauki matakin cafke wadanda ake zargin.

CP Dalijan, ya ce wanda ake zargin na farko, Mansur Haruna, wanda ya kasance kanin dan uwa ne ga marigayin, ya bayyana wa ‘yansanda yadda suka yi ta fama da Danjibga a lokacin da suke son sace shi, da kuma duk abin da ya faru da ya kai ga yanke hukuncin karshe na kashe shi.

A wata hira da Mansur Haruna, ya bayyana cewa kawunsa, Danjibga ne ya kore shi daga gidansa saboda ya lura da yana sata, inda ya kara da cewa, “Kafin ya kore ni daga gidansa, sau biyu na tuntube shi ina neman ya tsaya min na shiga aikin soja da kuma ‘yansanda, amma duk ya ki saboda mumunar dabi’a ta. Rundunar ‘yansandan su gabatar da takwarorin masu laifi daban-daban da suka kama don mika su kotu tare da hukunta su.

Leave a Reply

%d bloggers like this: