Gwamnatin Jihar Jigawa ta yabawa UNICEF kan ayyukan jin kai, kiwon lafiya, da tattalin arziki a jihar

0 205

Gwamnatin Jihar Jigawa ta yabawa Asusun Tallafawa Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) kan ayyukan jin kai da take yi sama da shekaru 30 da bayar da gudunmawa wajen inganta kiwon lafiya, zamantakewa da tattalin arziki a jihar.

Gwamnan jihar, Malam Umar Namadi, ya yi wannan yabon ne a lokacin da ya karbi bakuncin daraktar UNICEF ta kasa Madam Christian Monduate da tawagarta a ziyarar ban girma da suka kai gidan gwamnati dake Dutse.

Ya ce shiga tsakani na UNICEF shi ne tsoho da daidaiton sa hannun abokan tarayya a cikin jihar kuma ya canza labaran zuwa masu kyau.

A jawabinta yayin ziyarar, daraktar hukumar ta UNICEF Madam Christian Monduate ta yaba wa gwamnatin jihar bisa samar da yanayi mai kyau na shiga tsakani, “a gaskiya kuna bayar da hadin kai tare da nuna kwazo a duk wata yarjejeniya da mu.

Dangane da barkewar cutar diphtheria a halin yanzu a wasu jihohin Najeriya, inda jihar Jigawa kuma ta ba da rahoton mutane sama da 100 da ake zargin sun kamu da cutar tare da mutuwar mutane uku.  UNICEF ta ba da gudummawar allurar rigakafin diphtheria 3.1 don magance wannan annoba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: