Akalla ‘yan Najeriya miliyan 32 za su fuskanci wani yanayi mai kama da matsananciyar yunwa

0 170

Akwai yiyuwar akalla ‘yan Najeriya miliyan 32 za su fuskanci wani yanayi mai kama da matsananciyar yunwa a tsakanin watanin Yuni da Agustan bana matuƙar ba a ɗauki matakan gaggawa ba.

Wannan na ƙunshe cikin rahoton ‘Cadre Harminise’ na baya-bayan nan, wanda Kwamitin Kai Ɗauki na Ƙasa da Ƙasa IRC da gomman kungiyoyin kasa da ke aiki a yankin suka wallafa.

A cewar rahoton na IRC, adadin mutanen da za su fuskanci matsalar ƙarancin abinci a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar Afirka a wannan dan tsakani zai kai kimanin mutane miliyan 52 kwatankwacin kaso 12 cikin 100 na mutanen da aka tantance.

Ana sa ran kimanin mutane milyan 52 daga kasashe 17 da aka nazarta za su fuskanci gaba ta 3 zuwa ta 5 na wannan lokaci na karancin cimaka tsakanin watan Yuni zuwa Agusta.

Hakan na nufin cewar kaso 12 cikin 100 na al’ummar da aka nazarta za su sha wahala wajen samun abin da zasu ci.

Leave a Reply

%d bloggers like this: