Kungiyar kwadago na zargin jam’iyyar APC mai mulki da sanya ‘yan Najeriya cikin wahala

0 97

Kungiyar Kwadago ta soki ‘yan majalisar bangaren jam’iyyun adawa a majalisar dokokin kasar nan kan shirun da tace sun yi akan batun harajin da CBN ta bijiro dashi a baya-bayan nan.

Idan dai za a iya tunawa, CBN, a wata takardar da ya fitar a ranar 6 ga watan Mayu, ya umarci bankunan da ke aiki a kasar nan da su fara karbar harajin tsaro na yanar gizo kan hada-hadar kasuwanci a cikin makonni biyu daga ranar da aka bayar da sanarwar.

Da yake magana a lokacin da yake zantawa da manema labarai a jiya Juma’a, Shugaban kungiyar TUC, Festus Usifo, ya zargi jam’iyyar APC mai mulki da sanya ‘yan Najeriya cikin wahala, inda ya kara da cewa ‘yan majalisar jam’iyyun adawa sun kasa cewa komai akan batun.

Leave a Reply

%d bloggers like this: