An kama wasu mutane uku da ake zargi da satar awaki 48 a Babura da Kiyawa

0 151

Rundunar ‘yan sandan jihar Jigawa ta ce ta kama wasu mutane uku da ake zargi da satar awaki 48 a kananan hukumomin Babura da Kiyawa na jihar nan.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar nan, Ahmadu Abdullahi, ne ya shaida wa manema labarai a Dutse a jiya Alhamis cewa, an kama wadanda ake zargin ne a wani samame daban-daban tsakanin ranakun Litinin zuwa Talata.

Abdullahi ya ce biyu daga cikin wadanda ake zargin, mai suna Abdullahi Usman dan shekara 20 da Hassan Ado mai shekaru 22, ana zarginsu da hada baki da wani Tasiu Umar, wanda yanzu haka yake hannunsu, tare da sace awaki 26 da kudinsu ya kai Naira miliyan 1 da dubu dari uku.

Kwamishinan ya ce wani Hassan Ibrahim da ke kauyen Abari a Jamhuriyar Nijar a ranar 22 ga watan Janairu da misalin karfe 9 na safe ya je ofishin ‘yan sanda na Babura inda ya kai rahoton satar awakinsa na Naira miliyan 1 da dubu dari uku.

Kwamishinan ya ce wadanda ake zargin a yayin da ake yi musu tambayoyi sun amsa cewa sun sace awaki 26 sannan kuma sun tabbatar da cewa sun sayar da 18 daga cikin awakin ga Abdullahi Amadu na kauyen Kunyafa da Mustapha daga kauyen Madangana, duk a kan kudi N210,000. Kwamishinan ya kara da cewa wanda ake zargi na uku, mai suna Ado Buba mai shekaru 25, mazaunin kauyen Dundubus a Dutse, an kama shi da awaki 22 da ake zargin an sace.

Leave a Reply

%d bloggers like this: