An ceto wani mutum mai shekaru 37 da ke daf da rataye kansa

0 115

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta yi nasarar dakile wani mummunan lamari a jiya Alhamis inda ta ceto wani mutum mai shekaru 37 da ke daf da kashe kansa ta hanyar rataye kansa a kan bishiya.

Mutumin mai suna Saifullah Rabi’u ya ajiye takardar kashe kansa ne da ke nuni da cewa ya yanke kauna ne bayan ya ci bashin Naira miliyan 2 da ake bin sa wajen neman bizar kasar waje.

Kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Kano Saminu Abdullahi ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya rabewa manema labarai.

Ya ce sun samu Saifullahi Rabiu a cikin wani hali na rashin lafiya, yana kokarin kashe kansa ta hanyar rataye kansa a jikin bishiya.

A cikin takardar kashe kansa, Rabi’u ya bayyana dimbin bashin da ake binsa, inda ya bayyana cewa tuni ya mayar da kusan Naira 500,000 na kudaden da ya karbo. Ya koka da cewa kalubale da cin zarafi da yake fusknata daga masu karbar bashin ne  ya sanya shi  tunanin kashe kansa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: