An umurci shugabannin makarantu da su mayar wa dalibai kudaden da suka karba na WAEC/NECO

0 269

Hukumar tabbatar da ingancin ilimi ta jihar Benuwe, ta umurci shugabannin makarantun sakandaren jihar da su gaggauta mayar da kudaden da suka karba na gudanar da jarabawar WAEC/NECO ga daliban aji uku na Babbar sakandare.

Darakta Janar na hukumar Dr Francis Terna ne ya bayar da wannan umarni a ranar Alhamis, a lokacin da ya ziyarci wasu makarantu a Makurdi, babban birnin jihar.

Mista Terna ya zanta da wasu dalibai na aji uku na Babbar sakandaren a makarantun da ya ziyarta domin tantance kudin da suka biya a matsayin kudin jarabawar WAEC da NECO.

Ya kuma umurci dukkan makarantun da su bi ka’idojin da aka amince da su na biyan N5,000 ga kowane dalibi.

Ya kuma shawarci mahukuntan makarantun da su daina irin wadannan munanan dabi’u, inda ya kara da cewa rashin bin umarnin gwamnati zai sa su fuskanci hukuncin da ya dace.

Mista Terna ya ce gwamnatin jihar ta himmatu sosai wajen tabbatar da kyawawan halaye da kuma tabbatar da ingancin ilimi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: