Kungiyar kwadago ta soki matakan da Tinubu ke dauka kan tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya

0 99

A ranar Alhamis din da ta gabata ne kungiyar kwadago ta Najeriya ta yi suka ga matakan da shugaba Bola Tinubu ke dauka kan tabarbarewar tattalin arzikin da kasar ke fama da shi, wanda ta ce yana kara ta’azzara.

Shugaban kungiyar kwadagon, Joe Ajaero, wanda ya soki Tinubu kan sauye-sauyen tattalin arziki a taron tattaunawa na jaridar Daily Trust karo na 21 da aka yi a Abuja, ya gargadi shugaban kasa kan bin shawarar Bankin Duniya da Asusun Lamuni na Duniya.

Amma ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa, Mohammed Idris, wanda ya halarci taron, ya yi watsi da kamalan na Ajaero.

Ya kuma tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa nan ba da dadewa ba za su fara cin gajiyar sauye-sauyen da shugaban kasa ke yi.

Har ila yau, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da tsare-tsare, Mista Bayo Onanuga, a wata hira da ya yi da manema labarai, ya ce sauye-sauyen tattalin arzikin da shugaban kasa ya yi, na goyon bayan Najeriya ne da nufin daidaita tattalin arzikin kasar nan da kuma maido da darajar Naira da ke kara karyewa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: