An kama wasu mutum uku da ake zargi da laifin hada baki da yunkurin garkuwa da mutane

0 268

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wasu mutum uku da ake zargi da laifin hada baki da yunkurin garkuwa da mutane a jihar.

Kakakin rundunar, SP Ahmed Wakil ne, ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Bauchi.

Ya ce rundunar, a yaki da garkuwa da mutane da sauran munanan laifuka, na ci gaba da samun kyakkyawan sakamako a jihar.

Kakakin, ya ce mutumin ya yi barazanar sace shi ko kuma wani daga iyalinsa.

Bayan kwanaki kadan, wadanda ake zargin sai suka aike wa mutumin lambar asusun wani mai POS domin ya sanya kudin da suka nema, in ji Wakil.

A cewarsa, bayan samun bayanan sirrin, Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Mista Auwal Musa, ya umarci sashen binciken manyan laifuka (CID) da su binciki lamarin cikin nutsuwa. Kakakin ya bayan gudanar da bincike wadanda ake zargin sun amsa laifin da ake zargin su da shi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: