Yan bindiga sun kashe mutum 11 sun kuma yi garkuwa da mata 20 da kananan yara a jihar Zamfara

0 238

Al’ummar garin Gidan Zuma na ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara sun bayyana cewa ƴanbindiga sun je bisa mashina kusan 250 inda suka fara kashe mutum biyar a kusa da garin tare da kashe mutum shida a garin Gidan Zuma, da yin garkuwa da mata 20 da kananan yara.

Rahotanni sun ce maharan sun kai hari ne a ranar Asabar da Lahadi, wanda hakan ya jefa al’ummar yankin cikin fargaba ta rashin sanin abin da zai je ya dawo.

Mutanen yankin sun ce suna cikin halin ƙa-ƙa-ni-ka-yi saboda a kowa ne lokaci maharan ka iya sake afka masu, kuma ko da jami’an tsaro suka isa domin kai dauki, maharan sun tafi. Wani magidanci da ƴanbindigar suka tafi da matarsa da yaron da take goyo ya ce har cikin gida suka shiga suka tasa ta gaba.

Leave a Reply

%d bloggers like this: