An karrama shugaban kungiyar Miyetti Allah ta jihar Jigawa bisa jajircewa wajen sauke nauyin kungiyar

0 200

Kungiyar Fulani makiyaya ta Miyetti Allah Kautar Hore ta kasa ta karrama shugaban ta na jihar Alhaji Umar Kabir a matsayin shugaban da yafi kowanne jajircewa wajen sauke nauyin kungiyar.

Umar Kabir ya zama shugaban kungiyar Fulani mafi kulawa da hidimta alu’mmar Fulani, da kuma biyayya ga uwar kungiya ta kasa.

An gudanar da bikin karramawar ne a hedikwatar kungiyar dake Keffi a jihar Nassarawa ranar Talata data gabata.

Shugaban kungiyar na kasa alhaji Abdullahi Bello Bodejo ya mika lambar yabon ta kambun na zinare a ranar Talata, lura da zakukuranci, da gudunmawa wajen cigaban kungiyar a matakin jiha da kasa baki daya.

Kungiyoyi da sauran dai-daikun Fulani daga sassan nahiyar Afrika sun halarci taron.

Alhaji umar Kabir ya godewa allah bisa wannan nasara tare da godewa al’umar Fulani a jihar jigawa bisa wanzar da zaman lafiya da kuma goyon baya da suke bashi.

Leave a Reply

%d bloggers like this: