Sama da mutane 70 sun mutu sakamakon gobara da ta tashi a Johannesburg na Afirka ta Kudu

0 193

Ma’aikatan agajin gaggawa da ‘yan kwana-kwana a birnin Johannesburg na Afirka ta Kudu, sun ce sama da mutane 70 sun mutu sakamakon gobara da ta tashi a wani rukunin gidaje.

Jami’an sun ce mutane da dama sun ji mummunan rauni, kuma hukumomi sun ce ba a kai ga gane musabbabin tashin gobarar a ginin mai hawa biyar da ke wata unguwa a tsakiyar birnin ba.

Mai magana da yawun hukumar gaggawa Robert Mulaudzi ya ce wutar ta tashi ne a safiyar yau alhamis kuma ‘yan kwana-kwana sun yi nasarar fito da wasu mutane daga ginin.

Ya kuma ce wutar ta mamaye daukacin ginin, hakan ya zama abu mai matukar wuya ga ma’aikatansu, amma duk da hakan za a ci gaba da neman wadanda watakil suka maƙale a ginin.

Wani rahoto da kafar yaɗa labaran Afirka ta Kudu ya fitar na cewa da wuya a iya gano wasu gawarwaki, saboda konewar da suka yi kurumus.

Kawo yanzu dai an kai ga gano kimanin gawarwakin mutane 73 da suka mutu da kuma wasu 43 suka samu munanan raunuka sakamakon gobarar da tatashi a ƙasar Afirka ta Kudu.

Leave a Reply

%d bloggers like this: