Tinubu yayi ta’aziyyar gobara da ta shi a wani gini mai hawa biyar a Birnin Johannesburg

0 93

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sakon ta’aziyya ga gwamnatin kasar Afrika ta Kudu, biyo bayan wata gobara da ta shi a wani gini mai hawa biyar a Birnin Johannesburg.

Ta’ziyyar ta shugaba Tinubu na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin Ajuri Ngelale ya fitar.

Sanarwar tace shugaban kasa yayi addu’ar samun waraka ga wadanda suka raunata a sanadiyyar tashin wutar. Kazalika, shugaba Tinubu yayi fatan al’ummar kasar da gwamnatin da kuma sauran mutan afrika zasu taimakawa wadanda iftila’in ya shafa.

Leave a Reply

%d bloggers like this: