Sarkin Hadejia ya jinjinawa Gwamna Umar Namadi bisa gagarumin gyaran Asibitin Hadejia

0 187

Mai Martaba Sarkin Hadejia, Alhaji Dakta Adamu Abubakar Maje, ya kai ziyarar gani da ido Babban Asibitin Kwanciya na Hadejia domin duba aikin sabunta asibitin da gwamnatin Jihar Jigawa ke gudanarwa tare da tantance irin ci gaban da aka samu.

A yayin ziyarar, Sarkin ya zagaya sassa daban-daban na asibitin domin ganin yadda aikin ke gudana da kuma halin da marasa lafiya da ma’aikatan lafiya ke ciki.

Da yake jawabi bayan kammala ziyarar, Mai Martaba Sarkin Hadejia ya yabawa Gwamnan Jihar Jigawa, Malam Umar Namadi, bisa gagarumin aikin sabunta asibitin, wanda ya bayyana a matsayin mafi girman gyaran da aka taba yi wa asibitin tun bayan kafuwarsa a shekarar 1963.

Ya ce aikin zai taimaka matuka wajen inganta harkokin kiwon lafiya da samar wa al’umma ingantattun ayyukan jinya a yankin Hadejia da ma sauran sassan jihar.

Sarkin ya kuma yaba wa ma’aikatan asibitin bisa sadaukarwa da jajircewar da suke yi wajen kula da marasa lafiya, tare da bukatarsu da su ci gaba da nuna kwarewa da tausayi wajen gudanar da aikinsu.

Haka kuma, ya mika godiyarsa ga masu hannu da shuni da kungiyoyi masu zaman kansu da ke tallafawa harkokin asibitin, musamman Kwamitin Abokan Asibitin, bisa gudunmawar da suke bayarwa wajen bunkasa ayyukan lafiya.

Tun da farko, shugaban ma’aikatan jinya na asibitin, Alhaji Baba Ali, ya bayyana cewa irin wadannan ziyarce-ziyarcen na kara wa ma’aikata kwarin gwiwa da kuzarin aiki.

Ya ce hakan na kuma kara yawan amincewar al’umma da cibiyoyin lafiya, tare da jawo hankalin masu hannu da shuni su kara zuba jari da tallafawa bangaren lafiya domin inganta rayuwar jama’a.

Ya gode wa Mai Martaba Sarkin Hadejia bisa ziyarar da ya kai, yana mai cewa hakan ya nuna irin kulawar da masarautar ke bai wa harkokin kiwon lafiyar al’umma.

Leave a Reply