Gwamnatin Jigawa ta bai wa mata 300 da suka warke daga cutar yoyon fitsari tallafin naira miliyan uku

0 168

Gwamnatin Jihar Jigawa ta bai wa mata 300 da suka warke daga cutar yoyon fitsari (VVF) tallafin kudi na naira miliyan uku bayan kammala jinyarsu a Babban Asibitin Jahun.

Kwamishinar Harkokin Mata da Ci gaban Al’umma ta jihar, Hajiya Hadiza Tijjani Abdulwahab, ce ta bayyana hakan yayin bikin sallamar matan da aka yi wa tiyatar gyaran cutar a garin Jahun.

Ta ce kowace daga cikin mata 300 da aka sallama ta karbi buhun fulawa mai nauyin kilo 10, injin nika da kuma tallafin kudi na naira 10,000 domin taimaka musu wajen fara sana’a da inganta rayuwarsu bayan jinya.

A jawabinsa na maraba, Daraktan Babban Asibitin Jahun, Dakta Yusuf Sa’id Muhammad, ya bukaci matan da aka yi wa tiyata da su kiyaye dukkan shawarwari da umarnin likitoci domin tabbatar da dorewar lafiyarsu.

Shi ma Kodinetan Yaki da Cutar Yoyon Fitsari na Kasa a Jihar Jigawa, Anthony Daniel, ya bayyana cewa tun daga shekarar 2016 zuwa yanzu an yi wa kimanin mutum 3,700 tiyatar gyaran cutar yoyon fitsari a jihar.

A nasa jawabin, Shugaban Karamar Hukumar Jahun, Alhaji Jamilu Muhammad Dan-Malam, wanda mataimakinsa ya wakilta, ya sanar da bayar da tallafin naira miliyan daya ga matan da suka warke daga cutar.

Wasu daga cikin wadanda suka amfana da shirin, da suka hada da Khadija Abdullahi Jahun da Falmata Idris Barno da Halima Muhammad Kaduna, sun gode wa gwamnatin jihar da ma’aikatan lafiya bisa kulawar da suka samu da kuma nasarar tiyatar da aka yi musu.

Sun bayyana cewa tallafin da aka ba su zai taimaka musu wajen farfado da rayuwarsu da kuma samun hanyar dogaro da kai bayan shafe lokaci suna fama da matsalar cutar.

Leave a Reply