An kashe fitaccen shugaban kungiyar ISWAP na yammacin Afirka bayan wani hari da rundunar sojin saman Najeriya takai

0 77

An kashe fitaccen shugaban kungiyar ISWAP ta yammacin Afirka Sani Shuwaram, da sauran ‘yan ta’addar kungiyar bayan wani hari ta sama da rundunar sojin saman kasarnan takai a yankin Marte.

PRNigeria ta bayyana cewa jiragen  yakin Nigeria na Super Tucano da wasu jiragen na sojojin saman Najeriya ne suka aiwatar da harin bama-bamai a Gatari da kuma sansanin shugaban kungiyyar.

Shuwaram, an ce ya mutu ne sakamakon harbin bindiga da ya samu a lokacin da wasu jiragen yakin sojoji suka kai farmaki sansanin ISWAP da ke yankin Sabon Tumbuns na tafkin Chadi.

An kuma tabbatar da labarin kisan Shuwaram daga wata majiya mai karfi ta sirri wacce ta tabbatarwa PRNigeria.

PRNigeria ta kuma gano cewa an zabi Mallam Bako Gorgore a matsayin sabon shugaban kungiyyyar ta ISWAP wanda zai maye gurbin Shuwaram.

Amma da aka tuntubi kakakin rundunar sojin saman Najeriya, Air Commodore Edward Gabkwet, ya ki tabbatar da mutuwar Shuwaram.

Leave a Reply

%d bloggers like this: