Kungiyar malaman fasaha ta kasa (NAAT) ta umurci mambobinta da su fara yajin aikin gargadi na makonni biyu

0 47

Kungiyar malaman fasaha ta kasa (NAAT) ta umurci mambobinta da su fara yajin aikin gargadi na makonni biyu daga yau Litinin

Shugaban kungiyar, Ibeji Nwokoma, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a jiya, ya yi zargin gazawar gwamnatin tarayya wajen aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma a 2009.

Ya ce wa’adin kwanaki 14 da suka baiwa gwamnatin tarayya ya riga ya wuce, shiyasa suka tsindima yajin aikin.

Ya kuma ce sunkuma yanke wannan shawarar ne bayan Majalisar Zartaswar kungiyar ta kasa, ta yanke shawarar rufe dukkannin dakunan gwaje-gwaje, wuraren bita, dakunan karatu da kuma gonaki na tsawon lokacin yajin aikin gargadi.

Ya ce kashi 97.8 na rassan kungiyar ne suka kada kuri’ar amincewa da matakin shiga wannan yajin aikin.

Leave a Reply

%d bloggers like this: