Wasu masoya shugaban kasa Buhari sun koma jam’iyar NNPP a karamar hukumar Ringim ta nan Jihar Jigawa

0 139

Mambobin Wata Kungiyar Masoya Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyar APC sun koma Jam’iyar NNPP a karamar hukumar Ringim ta nan Jihar Jigawa.

Da yake jawabi a madadin wadanda suka koma Jam’iyar ta NNPP Jagoran masu sauyin shekar Malam Adamu Sankara, ya ce sun koma NNPP ne saboda gazawar Jam’iyar APC wajen cika Alkawarirrikan da ta daukawa Al’umma na kawo cigaba ga kasa.

Haka kuma ya ce Kungiyar sa ta Buhari Patriotic Support Organization sun amince su koma Jam’iyar NNPP tun daga kasa har sama domin cigaban Kasa.

Da ya ke Jawabi a lokacin karbar ta su Jagoran Jam’iyar NNPP na Jihar Jigawa kuma tsohon dan takarar gwamnan Jigawa karo na biyu Malam Aminu Ibrahim Ringim, ya ce an zabi Jagororin Jam’iyar na Kananan Hukumomi 27 da ke Jigawa ta hanyar sasanto.

Haka kuma ya ce an zabi Jagororin Jam’iyar 37 daga Kananan Hukumomin Jigawa.

Aminu Ibrahim Ringim, ya umarci sabbin Jagororin su kasance masu yin aiki tukuru domin ganin cewa Jam’iyar ta kai ga nasara a zaben shekarar 2023.

Leave a Reply

%d bloggers like this: