

- Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta rufe kamfanonin ruwa guda 10 a jihar Ondo bisa rashin bin ka’idoji - July 4, 2022
- Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar AA, Hamza Al-Mustapha, ya ce jam’iyyarsa ba za ta yi hadin gwiwa da mutanen da basu damu da makomar al’umma ba - July 4, 2022
- Yadda wani mutum ya kona matarsa bayan ya gama dukanta a jihar Ogun - July 4, 2022
Rundunar Yan sandan Jihar Jigawa ta shawarci Masu Motocin Hawa a Jihar nan su kasance masu yin taka-tsantsan biyo bayan yadda ake samun rahotan sace-sacen Motoci a sassa daban-daban na Jihar nan.
Kakakin Hukumar Yan sandan na Jihar nan ASP Lawan Shiisu Adam, shine ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Duste babban birnin Jihar.
Shiisu Adam ya gargadi mazauna Jihar nan masu motoci musamman a birnin Dutse su sanya Na’urorin karmata barayin Motoci a jikin motocin nasu biyo bayan yadda matsalar take karuwa.
A cewarsa, hukumar wanda ayyukan ta sun hada da kare lafiya da Dukiyoyin Al’umma, zata cigaba da fadakar da Al’umma musamman masu Motoci su dauki matakan da suka kamata domin tseratar da Motocin su.
Kakakin Hukumar ya bukaci masu motocin hawa a Jigawa su kasance suna ajiye motocin su a wuraren da suke da tsaro, da sanya na’urorin bibiyar motoci da kuma sauran matakan da zasu hana sace motocin.
Haka kuma ya ce hukumar zata cigaba da fadakar da Al’umma a duk lokacin da abubuwa kamar hakan suka taso.