An samu tashin hankali a Jihar Sokoto bayan da Gobara ta tashi a Kamfanin Siminti na BUA da ke Jihar wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar mutane 3 tare da raunata wasu 3n.

Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa NAN, ya rawaito cewa Gobara ta lalata wasu abubuwa masu muhimmanci a Kamfanin a sanadiyar faruwar lamarin.

Kamfanin NAN ya rawaito cewa lamarin ya faru ne a jiya da safe, kuma Gobarar na cigaba da kamawa a lokacin.

Manema Labarai sun rawaito cewa Jami’an hukumar kashe Gobara na gwamnatin tarayya da na Jiha suna aiki tukuru domin kashe wutar.

An bayar da rahotan cewa wutar ta kama ne a lokacin da wata tankar Mota take Loda Mai.

Kimanin mutane 3 ne aka bayar da rahotan mutuwar su a lokacin baya ga wasu mutane 3 da suka raunata sakamakon yadda Wutar ta fi karfin masu kashe Gobara a Kamfanin.

Kakakin Hukumar Kashe Gobar ana Jihar Sokoto Malam Nuhu Lawan, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce sun tura tawaga ta musamman zuwa wurin domin kashe ta.

Related Posts

Leave a Reply

%d bloggers like this: